Zikiran Bacci

Ya hada hannayansa sannan yai tofi a cikinsu sannan ya karanta Kulhuwa uku, Falaki Uku, Nasi Uku sannan ya shafi ko'ina ajinsa da zai iya, kuma zai yi hakan sau uku

Ayatl Kursiyyu

Ya karanta Amanarrasulu

Da sunanka ya Ubangiji na kwantar da hakarkarina, da kuma ikonka zan daga shi, idan ka amshi raina to kayi masa gafara, in kuma ka kyale shi to ka kiyaye shi da abinda kake kiyaye bayinka Nagartattu.

Ya ubangiji kaine ka halicci raina kuma kai ne zaka karbeta, a hannunka rayuwarta da Mutuwarta ya ke, in ka rayar da ita to ka kare ta in kuma ka karbeta to kayi mata gafara, Ya Ubangiji ina neman lafiya.

Allah ka tsare ni Azabarka ranar da zaka tashi bayinka

Da sunanka Allah Zan Mutu kuma da shi an rayu

Tsarki ya tabbata ga Allah (33) Godiya ta tabbat ga Allah (33) Allah shi ne mafi girma (33)

Ya ubangiji Ubangijin Sammai bakwai da kasa kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijin komai, wanda ya fitar da kwaya daga kalwadi, wanda ya saukar da Attaura da linjila da Qurani , ina neman tsarinka daga daga sharrin duk wani da makwankwadarsa take hannunka, ya Ubangiji kaine na farko babu kuma wani dake kafinka, kuma kaine na karshe babu wanda yake a bayanka, kumakaine bayyananne wanda babu wani abu a samansa, kuma kaine boyayyen da babu wani abu bayanka, ka biaya mana bashi kuma ka wadata mu daga Talauci

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya shar da mu, kuma ya bamu wurin zama, sabida akwai da yawa da basu da abinda zasu ci da inda zasu zauna

Ya Ubangiji Masanin fake da abinda yake fikli wanda ya halicci samai da kasa, kuma ubangijin komai da komai kuma mamallakinsa na shaida babu wani abin bauta da gaskiya sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin kaina da kuma sharrin shaidan da abokan tarayyarsa, ko kuma injawo kaina wani laifi ko kuma wani Musulmi

zai karanta Surat Assajda da kuma Surat Almulk

Ya ubangiji ni na mika wuya na gareka, kuma na bada al'amarina zuwa gareka, kuma na fuskantar da fuskata izuwa gareka kuma na jinginar da baya na izuwa gareka sabida kwadayi da kuma tsoronka, babu wurin buya ko matsera daga gare ka sai izuwa gare ka, nayi Imani da littafinka wanda ka saukar da Annabinka da ka aiko

API