Karatun sallar jana’iza
Ya Allah Ubangiji! Ka gafarta masa ka ji kansa ka yi masa afuwa ka yafe masa ka girmama mazauninsa ka yalwata makwancinsa, ka wanke shi da ruwa da kankara da sanyi, ka tsarkake shi daga kurakurai kamar yadda ka tsaftace tufafi da yake fari daga datti, ka janza masa gida wanda ya fi gidanshi (na nan duniya), da iyalai wadanda suka fi iyalansa, da mata wacce ta fi matarshi, ka shigar da shi aljanna kuma ka tsare shi daga azabar wuta da kuma azabar kabari.
Ya Allah Ubangiji! Ka gafartawa rayayyun mu da matattun mu da mahalartan mu da wadanda ba sa nan da kananan mu da manyan mu, da mazan mu da matan mu. Ya Allah Ubangiji! Duk wand aka rayar da shi daga cikin mu to ka rayar da shi akan musulunci, duk kuma wanda ka dauki ranshi daga cikin mu to ka dauki ranshi akan imani. Ya Allah Ubangiji! Kada ka haramta mana ladansa kuma kada ka batar da mu a bayansa.
Ya Allah Ubangiji! Lalle wane dan wane (sai ka fadi sunansa) yana wurinka, kuma yana neman kariyarka, to ka tsare shi daga azabar wuta, kuma kai ne ma’abocin cika alkawari, to ka gafarta masa kuma ka yi masa rahama, lalle kai ne mai yawan gafara mai yawan jinkai
Ya Allah Ubangiji! Bawanka dan baiwarka ya bukaci rahamarka, kai kuma mawadacine daga barin yi masa azaba, har in ya kasance mai kyautatawa to ka kara masa a kyautatawar ta sa, idan kuma ya kasance mai laifi ne to ka yafe masa.