Yada sallama

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya ce: “Ba zaku shiga aljannah ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so junan ku. Shin, ba na nuna muku wani abu da in kun yi shi za ku so junanku ba? Ku yada sallama a tsakaninku

Abubuwa uku duk wanda ya hada su hakika ya hada imani: Mutum ya yi adalci akan kansa, kuma ya yada gaisuwar sallama a cikin al’umma da yin kyauta a cikin rashin wadata

Daga Abdullahi bin Umar Allah ya kara masu yarda: Lallai wani Mutum ya tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Wane abu ne a cikin musulunci yafi alherin?. Sai ya ce ‘Ka ciyar da abinci kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba kasani ba”.

API