Addu’ar kunci

Babu wani Ubangiji sai Allah Mai girma kuma mai hakuri, babu wani Ubangiji sai Allah Ubangijin Al'arshi Mai girma, Babu wani Ubangiji Sai Allah Ubangijin sammai da Kasa kuma Ubangijin Al'arshi Maigirma.

Ya Ubangiji Rahamarka nake kauna, kada kabarni da kaina ko kiftawar Ido, kuma ka ingantamun sha'anina baki daya, Babu wani Ubangiji sai kai

Babu wani Ubangiji sai kai tsarki ya tabbata gareka lallai na kasance cikin wadanda suka zalunci kansa

( Allah Allah Shine Ubangijina bana hadashi da komai a cikin bauta )

API