Addu’ar Alkanut

Ya Ubangiji ka shiryar da ni cikin wadanda ka shiryar ka bmani lafiya cikin wadanda ka bawa, kuma kafi mun albarka cikin wadanda kayiwa, kuma ka kiyaye ni daga sharrin abinda ka kaddara, domin kaine mai hukunci kuma babu mai hukunta ka, domin bazai kaskanta ba duk wanda ya jibance ka, kuma bazai taba daukaka ba duk wanda ya kayi fushi da shi, tsarki ya tabbata a gareka ya Ubangiji kuma ka daukaka.

Ya Ubangiji lallai ina neman tsari da yardarka daga fushinka da afuwarka daga Ukubarka, kuma ina neman tsarinka daga gareka, ba zan iya kidanye yabo a gareka kawai kamar yadda ka yabi kanka.

Ya Ubangiji kaikadai muke bauta, kuma gareka muke Sa'ayi daga sassarfa, kuma muna tsoron Azabarka, Lallai cewa Azabarka ga kafirai mai riska ce, Ya Ubangiji Lallai muna neman taimakonka kuma muna neman gafararka, muna yaba maka alkairinka, kuma bama kafirce maka kuma muna yin Imani da kai, kuma muna kankan da kai a gare ka, kuma muna yanke hulda da duk wanda ya kafirce maka.

API