Addu’ar fara sallah

Ya Ubangiji ka nisanta tsakanina da tsakanin zunubaina kamar yadda ka nisanta tsakanin gabas da yamma, Ya Ubangiji ka tsarkake ni daga zunubaina kamar yadda ruwa yake wanke farar tufa daga datti, Ya Ubangiji ka tsarkake ni daga laifuka na da kankara da ruwa da kuma raba.

tsarki ya tabbata a gareka ya Ubangiji da kuma godiya a gareka kuma sunanka ya daukaka, haka girmanka ya daukaka, kuma babu wani Ubangiji bayanka

Na fuskantar da fuskata ga wanda ya halicci sammai da kasa kuma ina mai kan daidai, kuma ni bana cikin masu yin shirka, lallai cewa sallata da yankana da rayuwa ta da Mutuwa ta duk suna ga Allah ubangijin talikai, basahi da abokin tarayya kuma da haka aka umarce ni kuma ni ina cikin Musulmi, Ya Ubangiji kai ne Sarki wanda babu wani Ubangiji in ba kai ba kuma kaine Ubangiji na kuma ni bawanka ne, Na zalunci kaina kuma nayi furuci da laifi na ka gafarta min zunubai na baki daya lallai cewa kuma babu mai gafarta zunubai sai kai, ka sh iya shiriryar da ni ga mafi kyawun halaye kuma babu mai iya shirayawa izuwa mafi kyawun su sai kai , kuma ka kautar mun da Munanan halaye babu kuma mai iya kautar mun da su sai kai, amsawarka da rabauta, kuma dukkan Alkairi yana hannunka kuma sharri ba'a danganta shi izuwa gareka, Ni daga gareka nake kuma zuwa gareka zan koma, ka tsarkaka kuma ka daukaka, ina neman gafararka kuma ina tuba iuwa gareka.

Ya Ubangiji Ubangijin Jibirila da Mika'ila da Israfila, wandaa ya halicci sammai da kasa, masanin fake da abinda yake fili, kaine kake hukunci a tsakanin bayinka cikin abinda suke sabani akainkin abinda sukayi sabani a cikinsa, ka shirayar da ni cikin abinda aka yi sabani a cikin na gaskiya, da ikonka lallai kaine mai shiryarwa ga wanda kaso uwa tafarki madaidaici.

Allah shi ne mafi girma mai girma, Allah shi ne mafi girman mai girma kuma godiya mai yawa ga Allah, kuma godiya mai yawa ga Allah, kuma tsarki ya tabbata ga Allah Safiya da Maraice

Ya ubangiji dukkan yabo ya tabbata a gareka, kaine hasken sammai da kassai da abinda ke cikin su, dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine mai tsayar da sammai da kassai da abinda ke cikin su, [dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine ubangijin sammai da kassai da abinda ke cikin su] [dukkan yabo ya tabbata a gareka mulkin sammai da kassai da abinda ke cikin su naka ne] [ dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine mamallakin sammai da kassai ] [ dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine gaskiya, alkawarinka shi ne gaskiya, fadar ka ita ce ta gaskiya, haduwa da kai tabbas ne, aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce, annabawan ka gaskiya ne, muhammadu mai tsira da aminci gaskiya ne, tashin alkiyama gaskiya ne, ] [ yaa Allah gareka na mika wuya, kuma da kai kadai na dogara, kuma da kai kadai nayi imani, kuma zuwa gareka kadai na ke komawa, kuma saboda kai kadai nake jayayya, kuma gareka kadai na kai hukunci. Don haka ka gafarta mini abinda ya wuce, da abinda zai zo nan gaba, da abinda na boye, da abinda na bayyana, da abinda kai ka fini sanin abinda na aikata, kaine mai gabatarwa, kuma kaine mai jinkirtarwa, babu abin bautawa bisa can-canta sai kai kadai, kaine abin bauta ta babu abin bauta bisa can-canta sai kai. Babu dabara babu karfi sai ga Allah.

API