Addu’ar dawowa daga tafiya

Manzon Allah tsira da amincin Allah, su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga wurin yaki, ko aikin Hajji, ko Umra, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku sannan ya ce: “Babu abin bautawa da cancanta (da gaskiya) sai Allah, shi, shi kandai yake, ba shi da abokin tarayya, Mulki nasa ne shi kadai, kuma shi mai ikone a kan komai. Mu masu komawa ne, masu tuba ne, masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijin mu. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa Ya ruguza rundunomin kafirai shi kadai.

API