Daga cikin falalar tasbihi da tahmidi
Ma’ana: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Duk wanda ya ce; Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa, sau dari a rana, za a kankare masa zunuban sa ko da sun kasance kamar kumfar kogi ne.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Duk wanda ya ce: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah shi, Shi kadi, ba shi da abokin tarayya, dukkan mulki na sane kuma dukkanin yabo da godiya na sane, kuma shi mai iko ne akan komai. (So goma), to kamar wanda ya ‘yanta bayi hudu ne daga cikin ‘ya’yan Annabi Isma’il
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Akwan wasu kalmomi guda biyu masu saukin fada a harshe, kuma masu nauyi a kan mizani (na ayyukan ranar kiyama) masu soyuwa zuwa ga Allah Mai yawan jinkai, sune; “Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa, kuma tsarki ya tabbata ga Allah mai girma”.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Da zan fadi Tarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma shi ya fi soyuwa a gare ni daga dukkan abin da rana ta hudo a kansa.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi ya ce; “A yanzu dayan ku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowacce rana?, Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya ce; Ta yaya dayan mu zai aikata ayyuka dubu?. Sai Ma’aikin Allah ya ce: Ya yi Tasbihi dari, (yace: سُبْحَانَ اَللهِ) Tsarki ya tabbata ga Allah! Sau dari, sai a rubuta masa kyawawan ayyuka dubu ko a kankare masa zanubai dubu.
Ma’ana: “Duk wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma, tare da godiya gareshi. Za’a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna:
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ya Abdullah dan Kais! Ba na shiyar da kai ba ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai na ce. Shiryar da ni. “Sai ya ce: Ka ce:
“Babu dabara babu karfi sai da Allah.
Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Mafi soyuwar zance a wajan Allah su ne abubuwa hudu: Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma. Babu komai a gareka da wanne daga cikin su ka fara.
Ma’ana: Wani balaraben karkara ya zo wajen Manzon Allah, tsira da a mincin Allah su tabbata a gareshi, sai ya ce: Koya mini wadansu kalmomi da zan rika fada. Sai ya ce: “Ka ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Allah ne mafi girma, ina girmama shi girmamawa, kuma godiya ta tabbata ga Allah da yawa, tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah mabuwayi mai hikima. Sai mutumin ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, ni kuma nawa fa? Sai ya ce: Ka ce: Ya Allah Ka yi mini gafara, ka ji kai na ka shiryar da ni, ka azurtani.
Ma’ana: ldan mutum ya musulunta sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa sallah, sannan ya umurce shi ya rika addu‘a da wadannan kalmomi: “Ya Allah ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shiryar da ni, ka amintar da ni daga bala’i ka azurtani.
Ma’ana: Lalle mafificiyar addu’a ita ce fadin: “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah”. Kuma mafificin zikiri shi ne fadin: “Babu abin bautawa da cancanta sai Allah”.
Ma’ana: Ayyuka nagartattu masu wanzuwa su ne fadin: “Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Allah ne mafi girma, kuma babu dabara babu karfi sai ga Allah.