Daga cikin addu’o’in sallar rokon ruwa
				
				
				
				
									
						
						
						Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu ruwa mawadaci mai dadi, mai kosarwa mai anfani ba mai cutarwaba yanzu ba sai anjima ba.													
											 
									
						
						
						Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu, Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu, Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da mu.													
											 
									
						
						
						Ya Allah Ubangiji! Ka shayar da bayinka da dabbobinka, ka watsa rahamarka ka rayar da kasarka wacce ta mutu