. Addu’ar tafiya

Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Tsarki ya tabbata ga wanda yah ore mana wannan, kuma ba mu tkasance masu iya rijaya gareshi ba. Kuma lalle mu ga Ubangijin mu hakika masu komawa ne. Ya Allah lalle mu muna rokonta kyawawan al’amura da tsoronka a wannan tafiya ta mu, kuma muna rokonta aiki wand aka yarda da shi. Ya Allah ka sawwake mana wannan tafiya ta mu, ka nade mana nisanta. Ya Allah kai ne ma’abocin mu a cikin wannan tafiya, kuma kai ne halifan mu a cikin iyalan mu. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya bacin rai, da kuma mumnunar makoma ga iyali da dukiya. Idan ya dawo daga tafiyar ta sa, sai kuma ya fadi wannan addu’ar, ya kuma kara da cewa: Mu masu komawa ne, masu tuba masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijin mu.

API