Addu’a bayan tahiyar karshe

Ya Ubangiji ina neman tsari daga Azabar Kabari, da kuma Azabar Wutar Jahannama, da kuma fitinar Rayuwa da kuma ta Mutuwa, da kuma Sharrin Fitinar Dujal mai shafafen Ido

Ya Ubangiji ina neman tsari daga Azabar Kabari, da kuma fitinar Rayuwa da kuma ta Mutuwa, da kuma Sharrin Fitinar Dujal mai shafafen Ido kuma ina neman tsarinka daga sabo da kuma bashi

Ya Ubangiji ni lallai na zalunci kaina zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai kai kadai, kayi mun gafara gafara daga gareka kuma kaji kaina, domin kaine mai gafara mai jin kai,

Ya Ubangiji kayi mun gafara ga abinda na aikata, da wanda ban aikata ba da wanda na bayyyana da wanda ban bayyana ba, kuma kaine mafi sani da ni kuma kaine mai gabatarwa, kuma kaine mai jinkirtawa babu wani ubangiji sai kai

Ya Ubangiji ka taimakeni akan ambatonka da gode maka, da kuma kyautatawa a Ibadarka

Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsarinka daga yainwa, kuma ina neman tsarinka daga tsoro kuma ina neman tsarinka kada na koma kaskantacciyar rayuwa, kuma ina neman tsarinka, daga fitinar duniya da kuma Azabar Kabari

Ya Ubangiji ina rokonka Aljanna kuma ina neman tsarinka daga Wuta

Ya Ubangiji da iliminka na fake da kuma kudurarka ka raya ni matukar rayuwar ita tafi alkairi a gareni kuma ka karbi raina matukar Mutuwa ita ta fi Alkairi a gare ni, ya ubangiji ni ina rokonka kalmar gaskiya a cikin farin ciki da fushi, kuma ina rokonka Manufa cikin wadata da talauci kuma ina rokonka ni'amar da bata karewa, kuma ina rokonka farar idaniyar da bata yankewa, kuma ina rokonka yarda bayan kayi hukunci, kuma ina ronka sassanyar rayuwa bayan mutuwa, kuma ina rokonka, jin dadin ganin fuskarka da kuma shauki zuwa ga haduwa da kai ba tare da wata cuta ba ko cutarwa, ko kuma wata fitina mai batarwa, Ya Ubangiji ka kawatani da adon Imani kuma ka sanyani shiryayye mai shiryarwa

Ya Ubangiji ina rokonka Ya Allah cewa kai kadai kake wanda ake nufa da bukata wanda bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba, kuma bashi da kini mai tashin hanci, kayi mun gafara ga zunubai na lallai kai mai gafara kuma mai jin kai

Ya Ubangiji ina Rokonka cewa kai ne godita tabbata a gareka kai kadai babu wani Ubangiji sai, mai yawan baiwa, wanda ya kawata sama da kasa kuma ma'abocin girma da daukaka, ya wanda yake rayayye kuma tsayayye da kansa ina rokonka Aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.

Ya Ubangiji ina Rokonka cewa lallai na shaida babu wani Ubangiji sai kai makadaici abun nufi da bukata wanda bai haifa kuma ba'a haife shi ba kuma bashi da kini mai tashin hanci a gare shi.

API