Abinda zai fada domin maida sharrin miyagun shaidanu

Ma’ana: Ina neman tsari da Kalmomin Allah cikakku, waddanda wani bawa na gari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da Allah ya halitta, Ya Samar da shi daga babu Ya fari haliltarsa, haka kuma daga sharrin abin da yake saukowa daga samaa da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gareta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da Alheri Ya Allah mai yawan rahama.

API