Addu’ar Sujjada

Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Madaukaki

Tsarki ya tabbata a gareka Ubangijinmu da godiya a gareka, Ubangiji kayi mun gafara

Tsakakke, Mai yawan tsarki,, Ubangijin Mala'iku da kuma Ruhi mai tsarki (Jibril)

ya Unagiji gareka nake Sujada kuma da kai nayi Imani kuma fuskata tayi Sujada ga wanda ya halicce ta kuma ya suranta ta kuma ya tsaga jinta, da ganinta, tsarki ya tabbata ga Maficin iya halitta

Tsarki ya tabbata ga Ma'abocin isa, da Mulki, da girma, da Daukaka

Allah ka gafarta mun zunubaina baki daya, karaminsa da babbansa, na farkonsa da na karshensa, bayyananne da kuma boyayyensa

Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsarinka daga fushinka ta hanyar yardarka da kuma afuwarka daga Ukubarka, kuma ina neman tsarinka daga gareka, kuma bana kidanye yabo a gareka, kai dai kamar yadda ka tabbatarwa kanka.

API