Abinda ake karantawa yara domin neman tsari
Ma’aikin Allah (s.a.w) ya kasance yana yi wa Alhasan da Alhusaini addu’ar neman tsari yana cewa: Ina nema muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkanin shaidani da canfecanfe, haka kuma daga dukkanin ido memugun nufi.