Addu’ar Sallar Istahara

abir ya ce: Manzon Allah ya kasance yana koya mana Istikhara cikin dukkan kamar yadda yake koya mana Ayoyin Alqurani yace: idan dayan ku yai nufin yin wani al;amari to yayi sallah rakaa biyu wacce ba ta farillah ba sannan ya ce: Ya Ubangiji ina neman zabinka da Iliminka kuma ina neman iko da ikonka kuma ina nema daga falalarka mai girma, domin kai ne mai iko kuma kai ka sani ni ban sani ba idana kasan cewa wannan al'amari -sai ya fadi bukatarsa- alkairi ce a gareni a cikin Addini na da karshen al'amari na - ko ya ce : Yanzu da na gaba- to ka kaddara mun shi kuma ka saukake mun shi sannan ka sanya mun albarka a cikinsa, idan kuma kasan wannan alamari sharri ne a gareni a cikin Addini na da karshen al'amarina - ko yace yanzu da nan gaba- ka kautar mun da shi kautar mun da shi kuma ka kaddara mun alkairi duk inda ya kasance sannan kuma ka sanya mun yarda da shi.

API