Falalar gaida maralafiya
Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce:
Idan mutum ya gaida dan’uwansa musulmi da ba shi da lafiya, to ya tafi ne akan hanyar aljanna har ya zauna, idan ya zauna kuma rahama ta lullube shi. Idan da safe ne mala’iku dubu saba’in ne za su yi masa salati har yamma ta yi. Idan kuwa da yamma ne to mala’iku dubu saba’in za su yi masa salati har gari yaw aye