Zikiran safe da yamma

Ya karanta Ayatal Kursiyyu

Ya karanta Kulhuwa da falaki da Nasu ( Sau Uku )

un wayi gari kuma mulki na Allah ne kuma godiya ta tabbata ga Allah Babu wani Ubangiji sai shi shi kadai bashida abokin tarayya kuma godiya tasa ce kuma mai iko ne akan komai Ubangiji ina rokon ka Alkairin wannan rana da alkairin abinda yake bayanta kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan rana da abinda yake bayanta Ubangiji ina neman tsarinka daga Kasala da Mummunan girman kai, Ubangiji ina neman tsarinka daga Azabar wuta da kuma Azabar Kabari

Ya Ubangiji dakai muka wayi gari kuma dakai mukayi yammaci, kuma dakai muke Rayuwa kuma dakai muka mutuwa kuma gareka muke tashi

Ya Ubangiji kaine ubangiji na babu wani Ubangiji sai kai kai ka halicce ni kuma ni bawanka ne kuma ina nan akan alkaarinka gwargwadon iko ina neman tsarinka daga abinda nayi kuma ina furuci da ni'amar da kayi mun kuma ina furuci da zunubaina kayi mun gafara babu mai gafarta zunubai sai kai kadai

Ya Ubangiji Ni na wayi gari ina shaidawa da kai kuma ina shaidawa da wadanda suke dauke da Al'arshinka da Mala;ikunka da baki dayan halittunka babu wani Ubangiji sai kai kadai baka da abokin tarayya, kuma Annabi muhammadu Bawanka kuma kuma Manzonka ( Sau Hudu)

Ya Ubangiji abinda Muka wayi gari da shi na Ni'ama ko wani daga cikin halittarka to daga gareka ne kai kadai bakada abokin tarayya, godiya ta tabbata a gareka kuma da yabo

Ya Ubangiji ka bani lafiya a jikina Ya Ubangiji ka bani lafiya cikin jina ya Ubangiji ka bani lafiya cikin gani na Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga Kafirci da kuma talauci, kuma ina neman tsarin ka daga Azabar kabari babu wani ubangiji sai kai ( Sau uku )

Allah ya ishe ni Babu wani Ubangiji sai shi gare shi na dogara kuma shi ne ubangijin Al'arshi mai girma ( Sau bakwai )

Ya Ubangiji ina rokonka afuwa da lafiya a Dauniya da lahira Ya Ubangiji ina rokonka afuwa da da lafiya, a cikin Acikin Duniya ta da Ahalina da Dukiya ta Ya Ubangiji ka Suturta Al'aura ta kuma ka amintar da ni abinda nake tsoro, Ya Ubangiji ka kiyaye ni a gabana da baya na, da dama na da haguna da sama na da kasa na kuma ina neman tsari da girmanka kada a hallaka ni ta karkashina

Ya Ubangiji Masanin fake da fili wanda ya halicci sama da kasa ubangijin komai kuma mai mulkinsu na shaida babu wani ubnagiji sai kai ina neman tsarinka daga sharrin kaina da sharrin shaidan da mataimakansa ko kuma inyi wani zunubi ko injawo shi ga wani Musulmi

Da sunan Allah wanda babu abinda yake utarwa da fadin sunansa a cikin sama ne ko kuma a kasa kuma shi mai ji ne masani

Na yarda da Allah shi ne Ubangiji kuma Musulunci shi ne Addini kuma Annabi Muhammadu shi ne Annabi (Sau Uku)

Ya rayayye tsayyae da kansa ina neman agajinka da rahamarka ka inganta mun al'amura na baki daya kuma kada ka barni da kaina ko daidai da kiftawar Ido

Mun wayi gari kuma mulki yana hannun Allah Ina rokonka Alkairin wannan rana budinta da Nasararta da haskenta da albarkarta da kuma shiriyarta, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin duk abinda yake cikin ta da sharrin abinda yake bayanta

Mun wayi gari akan turbar Addinin Musulunci, kuma kan kalmar tsarkake Addini kuma kan Addinin Annabinmu Muhammad kuma kan tafarkin Babanmu Annabi Ibrahim wanda ya tsaya kyam kan Addini bai kasance cikin masu shika ba

Tsarki ya tabbata ga Allah da kuma godiya ( Sau dari )

Babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah shi kadai wanda bashi da Abokin tarayya Mulki nasa ne haka ma godiya kuma shi mai Iko ne akan komai ( Sau goma) ko ( Sau daya in ya gaji)

Babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya Mulki nasa ne haka ma godiya kuma shi mai iko ne akan komai

Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarsa, yawan halittarsa da kuma yardarsa, da kuma nauyin Al'arshinsa da kuma yawan Kalmominsa, ( Sau Uku safe )

Ya Ubangiji ina rokonka Ilimi mai amfani, da Arziki mai albarka, da aiki karbabbe ( Da safe)

Ina neman gafarar Allah kuma ina tuba izuwa gare shi ( Sau dai)

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta

Yace: Allah kayi salati da tsira ga Anabinmu Muhammad ( Sau goma )

API