Zikiri a Muzdalifa

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi Ya hau taguwarsa mai suna Alkaswa’a har ya zo Mash’aril Haram (Muzdalifa), sai ya fuskanci alkibla ya yi addu’a ga Allah,ya yi kabbara ya yi hailala, ya kadaita Allah, bai gushe ba a tsaye yana addu’a har sai da gari ya waye sosai, sannan ya dauki hanya kafir rana ta fito.

API