Addu’ar ruku’i

( Tsarki ya tabbata ga ubangiji na mai girma ). sau uku.

(Tsarki ya tabbata a gareka ya Allah ! ya ubangijin mu tare da godiya gareka, ya Allah ka gafarta mini).

(Ubangi abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abinda bai kamace shi ba, ubangijin mala`iku da jibrilu).

( Ya Allah a gareka nayi ruku`u, da kuma kai kadai nayi imani, kuma gareka na mika wuya, ji na ya kas-kanta gareka, da gani na, da kuma kwakwalwa ta, da kashi na, da jijiya ta, da abinda kafafuwa na ke dauke da su.

(Tsarki ya tabbata ga Ma''abocin Mulki da halittu, da kuma girma da Daukaka)

API