Zikirai bayan sallamewa daga sallah

Ina neman gafarar Allah (3) Ya Ubangiji kai ne Aminci kuma daga gareka amincin ya ke, ka daukaka ya Ma'abocin girma da daukaka,

Babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kadai kuma bashi da abokin tarayya kuma godiya ta tabbata a gare shi, kuma shi mai iko ne akan komai( 3) Ya Ubangiji babu mai hana abinda ka bayar kuma babu wata amfanarwa da wanda yake da girma yake yi daga girmanka.

Babu wani Ubangiji da sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya mulki naka ne kuma godiya ta tabbata a gareka kuma kai mai iko ne akan komai, babu tsimi kuma babu dabara sai na Allah babu wawani ubangiji sai Allah kuma kuma shi kadai muke bautawa, ni'ama tasa ce haka falala kuma shi ne wanda kyakkyawan yabo ya tabbata a gare shi, Babu wani Ubangi sai Allah muna masu tsarkake shi kuma Addini nasa ne koda kafirai sunki kuwa

Subhanallahi walhamdu lillah wallahu Akbar (33) kuam babu wani abin bauta sai Allah shi kadai wanda bashi abokin tarayya, Mulki nasa ne haka kuma godiya, kuma Mai iko ne akan komai

Ya karanta Kuhuwa da Falaki da nasi a bayan kowace sallah

Ya Karanta Ayatal Kursiyyi a bayan kowace Sallah

Babu wani Ubangiji Sai Allah shi kadai kuma bashio da Abokin tarayya, kuma gareshi godiya take kuma yana rayawa kuma yana kashewa kuma shi ,ai iko ne akan komai Sau goma bayan Sallar Magriba da kuma Asuba

Ya Ubangiji ina rokonka Ilimi mai amfani da kuma Arziki mai tsafta da aiki karbabbe

API