Falalar salati ga Annabi ( S.A.W)

Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:“Wanda ya yi salata daya agare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi”.

Kuma Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko ina kuka kasance

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba”.

Kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ‘Allah yana da wadan su mala’iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al’umma ta’.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa”.

API