Zikiran kiran sallah

Ma'ana: Musulmi zai fadi dukkan abinda mai kiran ‎sallah ya ce, saidai idan mai kiran sallar ya ce: ‎

Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini. Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Zaiyi Sati ga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi bayan ya gama bibiyar mai kiran Sallah

Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.

Yana Addu'a ga kansa tsakanin kiran Sallah da Iqama sabida Addu'a a wannan lokacin

API