Addu’ar maralafi da ya fidda rai da tashinsa
Ya Allah ka gafarta mini ka kuma yi mini rahama, ka riskar da ni da tawaga madaukaka
Annabi ya sanya hannunsa cikin ruwa lokacin Mutuwarsa yana shafar fuskarsa da su yana cewa : Babu Sarki sai Allah lallai Mutuwa tanada magagi
Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah shi ne mai girma, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, gareshi kadai mulki yake kuma dukkan godiya ta tabbata a gareshi, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, babu karfi kuma babu dabara sai ga Allah.