Addu’ar tafiya masallaci
Ma’ana: Ya Allah ka sanya haske acikin zuciya ta, da haske ga harshe na, da haske ga ji na, da haske a gani na, da haske a karkashi na da haske a sama na, da haske a dama ta da haske a hagu na da haske a gaba na da haske a baya na, ka sanya haske a cikin raai na, ka girmama mini haske na, ka girmama haske, ka sanya ni na zama haske, ka sanya haske a cikin jijiyoyi na da haske acikin nama na, da haske a cikin jini na, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fata ta. Ya Allah! Ka sanya mini haske a cikin kabarin na, da haske a cikin kasusuwa na, ka kara mini haske, ka kara mini haske, ka kara mini haske ka bani haske akan haske.