Addu’ar tsayuwa a safa da marwa

Manzon Allah tsira da amiacin Allah su tabbata a gare shi yanyin da ya kusanto dutsen Safa da sai ya karanta: “Lallai Dutsen Safa da Marwa suna daga cikin alamomin da Allah ya sanya na addinsa’’. Ina farawa da abinda Allah ya fara da shi, sannan ya fara da dutsen Safa, ya hau shi har saida ya hango dakin Allah, sai ya fuskaci alkibila, ya kadaita Allah kuma girmama shi sai ya ce: Allah ne mai girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma. Bayan haka sai ya kara da hailala ya ce: Babu wani abin bauta da cancanta sai shi, shi kadai yake ba shi da abokin tarraya mai iko ne a kan komai, babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake. Allah ya gaskata alkwarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza randunonin kafirai shi kadai. Sannan ya karanta hakan yana mai addu’a a tsakanin haka: sai kuma ya fadi wannan addu’a misali sau uku. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan dutsen Safa.

API