Addu’ar wanda ya ji tsoron mai mulki

Ya Ubangiji Ubangijin Sammai bakwai , Ubangijin Al'arshi Mai girma, ka zamanto mun Kariya daga wane dan wane, da kuma rundunarsa daga cikin Haluttunka, kan daya daga cikinsu yayi mun Ta'adanci, wanda duk ka tsare to ya daukaka, kuma yabonka ya ya daukaka, kuma babu wani Ubangiji Sai kai.

Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi girma daga halittarsa baki daya, Allah shi ne mafi girman abinda nake tsoro kuma nake kiyaya, ina neman tsarin Allah wanda babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai shi, wanda yake rike da sammai bakwai da basu fado kasa ba sai da izininsa, daga sharrin bawanka wane, da rundunarsa da mabiyansa da yan korensa, na daga Aljanu da Mutane, Ya Ubangiji ka zamar mun mai kariya daga sharrinsu, Yabonka ya daukaka, kuma kariyarka ta girmama, kuma sunanka ya tsarkaka, babu wani Ubangiji in ba kai ba.

API