Abinda zai yi wanda abin farin ciki ya zo masa
				
				
				
				
									
						
						
						Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan wani al’amari da yake faranta masa rai, ko ake murna da shi yazo masa, sai ya fadi yana mai sujjada domin godiya ga Allah mai tsarki da daukaka.