Zikirin tashi daga bacci

Ma’ana: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauke ranmu (nufashi), kuma gare shi ne makoma take .

Ma’ana: Babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya na sane, kuma shi akan dukkan komai mai iko ne, tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu wanda ya cancan abauta masa sai Allah, Allah mai girma, babu wata dabara kuma babu karfi sai ga Allah madaukaki mai girma, Ubangi ka gafarta mini.

Dukkan godiya ta tabbata ga wanda ya bani lafiya a jikina, kuma ya dawo mini da raina kuma ya bani izinin ambaton sa .

Ayoyin guma 11 na karshe suratul Al imrana. (wato fadin Allah mai girma da daukaka): Ma’ana: Lalle a cikin halittar sammai da kasa, da kuma jujjuyawar dare da yini to akwai abubuwan la’akari ga ma’aboda hankula. Su ne wadanda suke anbaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma gefan jukkunansu, kuma suna tunani a halittar sammai da kasa, (suna cewa Ya) Ubangijin mu ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata a gareka to ka tsare mu azabar wuta. (Ya) Ubangijn mu! Lalle ne kai duk wanda ka shigar da shi wuta to hakika ka tozartar da shi, kuma kafirai ba su da mataimaka. (Ya) Ubangijin mu! Lalle ne mu mun ji maishela yana kira akan ku yi imani da Ubangijinku to mun yi imani, (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana zunuban mu, kuma ka kankare mana laifukan mu kuma ka dauki rayukan mu tare da mutanan kwarai. (Ya) Ubangijin mu! Kuma ka ba mu abinda ka yi mana alkawarinsa akan (har sunan) Manzanninka, kuma kada ka kunyata mu ranar alkiyama, lalle ne kai ba ka saba alkawari. Sai Ubangijin su ya amsa musu (cewa) lalle ni ba na tozartar da aikin mai aiki daga cikinku daga namiji ko mace, sashinku daga sashi, to dukkan wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajansu aka kuma cutar da su akan hanya ta, kuma suka yi yaki kuma aka kashe su hakika zan kankare musu laifukansu kuma hakika zan shigar da su gidaje na aljanna da koramu suke gudana daga karkashinsu (wannan) ladane daga wurin Allah, kuma Allah a wurinsa ne kyakkyawan lada yake. Kada jujjuyawar da kafirai suke yi a garuruwa ya rudar da kai. Jin dadine kadan, sannan makomarsu jahannama, kuma ta yi muni ta zama shinfida. Saidai dukkanin wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu suna da gidaje na aljanna da koramu suke gudana daga karkashin su masu dawwamane a cikinta, garace daga wurin Allah, kuma abinda yake a wurin Allah shi ne ya fi ga mutanan kwarai. Kuma hakika akwai daga cikin wadanda aka baiwa littafi wadanda tabbas suna yin imani da Allah da kuma abinda aka saukar zuwa gareku da kuma abinda aka saukar zuwa garesu suna masu kankan-da-kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da kudi kadan, wadannan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, lalle Allah mai saurin hisabi ne. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri ku cije kuma ku yi dako ku ji tsoron Allah domin ku rabauta. (Suratu Ali Imran, aya ta:190-200).

API