Istigfari da tuba

Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ina rantsuwa da Allah, lalle ni ina neman gafarar Allah kuma ina tuba gare shi a kowacce rana sama da sau saba’in.

Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku tuba zuwa ga Allah domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare shi sau dari.

Ma’ana: Ina neman gafarar Allah, wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, Tsayayye (wanda kowa ya tsayu da shi), kuma ina tuba zuwa gare shi. Allah zai gafarta masa zunuban sa ko da ya gudu daga fagen fama ne.

Ma’ana: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Mafi kusanci da Allah yake kasancewa da bawansa shi ne a tsakiyar karshen darene. Don haka Idan kana da ikon kasancewa cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin to ka kasance.

Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mafi kusancin da bawa zai kasance da Allah Ubangijinsa shi ne lokacin da bawansa yake sujada, don haka ku ya waita addu’a. (A cikin sujada)

Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce. “Hakika a kan lullube zuciyata, kuma ni ina neman gafarar Allaha sau dari a rana.

API